ABNA24 : A ranar Juma’ar da ta gabata an yi wata tattaunawar kwamitin ta hanyar bidiyo daga nesa da ya hada kasashen Iran, Birtaniya, Jamus, Farace, sai kuma China da Rasha, sai kuwa tarayyar turai.
Araqchi ne yake wakiltar tawagar Iran a taron da za a yi a yau, wanda ci gaba ne na wanda aka yi a ranar juma’ar da ta gabata. A ranar Lahadin da ta gabata, mataimakin ministan harkokin wajen na Iran ya shaida wa manema labaru cewa; Taron na Vienna zai mayar da hankali ne akan tattauna hanyoyin da za a dauke wa Iran takunkuman da aka kakaba ma ta.
Tun da fari dai Iran ta bayyana sharadinta na komawa aiki da yarjejeniyar Nukilyar wanda shi ne dauke ma ta takunkumi.
342/